ada

Breaking News

AN TSINCI JARIRI A WANI KANGO A GARIN AMBURSA A JIHAR KEBBI

An Tsinci Jariri A Wani Kango A Garin Ambursa Ta Jihar Kebbi
Hukumar Hisba ta jihar Kebbi na bada sanarwar an kawo mata wani yaro jariri sabon haihuwa wanda aka ajiye a cikin wani kangon gida a garin Ambursa dake karamar hukumar mulki ta Birnin Kebbi.
An tsinci jaririn ne cikin buhu, yana kuka, a ranar Juma'ar da ta gabata da misalin karfe 2:30 yamma.
Hukumar na kira ga jama'ar yankin na Ambursa da duk wanda ya san uwar wannan yaro ko kuma wata da ake tuhuma da nata ne da a sanar da hukuma don daukar matakin da ya dace.
Sanarwar na dauke da sa hannun mataimakin shugaban Hisba na jihar Kebbi, Alhaji Mamuda Geza
RARIYA

No comments

Rubuta ra ayin ka