AN SACE DALIBAI DA MALAMAN SU A JIHAR OGUN

Wasu ‘yan bindiga a jahar Ogun sun afkawa wata makarantar kasa da kasa inda suka sace dalibai biyar da malamansu biyu.
Akasarin daliban makarantar dai ‘yan kasar Turkiya ne.
Rudunar ‘yan sanda jahar ta sha alwashin nemo dalibai da malaman, da kuma cafke wadanada ke da hannu a aika aikar.
Satar mutane dai ya zama ruwan dare a Nijeriya musammam ma a yankin kudancin kasar nan, inda ‘yan bindiga suka saba kama ma’aikata ‘yan kasashen waje domin samun kudin fansa.
A watan Satumbar da ta gabata ma, ‘yan sanda a jahar ta Ogun sun ceto wasu ‘yan kasar China da aka sace, wadanda ke aiki a wani kamfanin fasa dutse.

AL'UMMATA
AN SACE DALIBAI DA MALAMAN SU A JIHAR OGUN AN SACE DALIBAI DA MALAMAN SU A JIHAR OGUN Reviewed by on January 15, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.