An kama ‘yan fashi fiye da 400 a Kaduna

Yansandan a jihar Kaduna da ke a Arewacin Najeriya sun sanar da cafke ‘yan fashi sama da 400 wadanda ake zargi da laifin yin garkuwa da mutane da kuma satar shanu a cikin shekarar 2016.
Kwamishina ‘yansandan jihar, Mista Agyelo Abeh ne ya tabbatar da kama mutanen ya kuma shaida cewa sun kwato muggan makamai sama da 100 daga hannu ‘yan fashin.
Mista Agyelo ya ce tuni aka mika 384 daga cikin wadanda aka kama gaban kuliya, yayin da ake ci gaba da binciken sauran.
Matsalar satar shanu da kuma yin garkuwa da mutane ya zama ruwan dare gama gari a Najeriya a shekarun baya bayan nan.
RFI Hausa
An kama ‘yan fashi fiye da 400 a Kaduna An kama ‘yan fashi fiye da 400 a Kaduna Reviewed by on January 28, 2017 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.