AN KAMA WANI MUTUMIN DA YA BOYE HODAR IBLIS NA BILIYAN 1.9 A SAHUN TAKALMA

Jami’an hana safarar miyagun kwayoyi a Nijeriya NDLEA sun kama wani mutum dan Nijeriya mai shekaru 34 dauke da kilo 9.150 na hodal Iblis.
An kama mutumin mai suna Okolo Emenike ne yayin da yake yunkurin shigo da hodar daga kasar Brazil inda ya boye su a cikin sahun wasu takalma da aka kunshe a cikin kwalaye.
Kwamandan hukumar, Hamisu Lawan ya shaidawa manema labarai a tashar jirgin sama na Abuja cewa farashin hodar iblis din ya kai pam biliyan 3.8 wanda ya yi dai dai da kimanin Naira bilyan 1.9.
Ya ce wannan mutum shi ne mutum na karshe da suka kama a shekarar 2016.
Da yake fadin yadda abun ya faru, Okolo ya bayyana cewa wani abokin sa ne ya bashi naira miliyan 1 domin ya taimaka masa wajen shigo da hodar iblis din Nijeriya.
Ya ce da ma can ya tafi kasar Brazil ne domin ya nemi abun yi sai dai hakan bai yiwu ba, al’amarin da ya sanya shi cikin matsin rayuwa. Ya kara da cewa ya na da niyyar amfani da miliyan dayan ne wajen sanya jari.
(AL'UMMATA )

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN