AN CAFKE MATAIMAKIN KARAMAR HUKUMAR BAMA A BISA ZARGIN TAIMAKA WA BOKO HARAM

Kwamandan Rundunar Sojan Nijeriya da ke karkashin Ofireshon Zaman Lafiya Dole Manjo Janar Lucky Irabor ya tabbatar da cafke Mataimakin Shugaban Karamar hukumar Kaga da ke jahar Borno bisa zarginsa da tallafa wa mayakan Boko Haram.
Irabo ya fadi haka ne a wani taron manema labarai a yau Alhamis a Hedikwatar rundunar da ke Maiduguri.
Ya bayyana cewa mataimakin karamar hukumar Kagan yanzu haka ya na amsa tambayoyi.
Wannan al’amari dai ya zo ne a dai-dai lokacin da rundunar ta tabbatar da cafke Shugaban Karamar Hukumar Mafa, Shettima Lawan da Mahaifinsa bisa zargin tallafawa mayakan Boko Haram.
(AL'UMMATA)

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN