Abubuwan da za ki yi yayin da kike soyayya da saurayin ki

Bayan kin Fahimci Saurayin ki wane irin mutun ne kuma hankalin ki ya kwanta dashi, akwai abubuwa da dama da ya kamata ki kula dasu a ya...

Bayan kin Fahimci Saurayin ki wane irin mutun ne kuma hankalin ki ya kwanta dashi, akwai abubuwa da dama da ya kamata ki kula dasu a yayin da kuke soyayya. Ga wasu daga cikin su:
Wace irin So zaki nuna masa
Yan Mata da dama suna wani kuskure a Rayuwa domin kuwa suna nuna wa samarin su soyayya irin wacce ya kamata su nuna wa Mazajen su. Wannan ba karamin kuskure bane, domin kuwa akwai banbancin soyayyar da zaki nuna wa mijin ki da kuma Sauryanki (wanda kike so ki aura). Misali: Duk irin son da kike yiwa saurayi kada ki kuskura ki bari ya Taba ki, domin kuwa ba huruminsa bane.
Yadda zaku rika yin hira
Ki tabbatar da cewa Duk Soyayyar da zaki yi da Saurayi kinyi ta yadda Musulunci ya umurce ki kiyi, Musamman Hira. Domin kuwa duk wacce ta bi abunda shari’a ta umurceta dashi zata samu Kwanciyar Hankali a rayuwarta da Aure. Ki tabbatar da a koda yaushe kuna da wurin da kuke hira wanda Iyayen ki suka yadda dashi sannan kuma ki guji Hira da Saurayi a cikin Mota musamman Mai bakin Gilas. Duk shedan yana amfani da dama ya cusa muku sha’awar Juna , wanda kuma hakan Matsala ne a yayin da kike soyayya.
Tsawon Lokacin da ya kamata kuyi kuna soyayya
A yayin da kika san cewa gidan ku a shirye ake da a miki aure kuma Saurayinki bai shirya ba toh ya kamata ki Fahimci cewa Idan fa Kika bata lokaci jiran wanda bai shirya naki lokacin ke tafiya ba nasa ba, domin kuwa Namiji baya saurin Tsufa. Amma a matsayin kin a budurwa akwai wasu shekaru da zaki kai da ba kowane Saurayi zai yarda ya aure ki ba. Dan Haka kada ki yarda kuyi shekaru masu Yawa kuna soyayya domin kuwa hakan Zai iya kawo cikas.
Ki rika Rufe Jikinki
Kada ki kuskura ki rika shiga irin wacce zata sa Saurayinki ya rika Sha’awar ki, domin kuwa Shedan zaiyi amfani da wannan damar wajen kawo wata matsala. Yana da kyau kije fira cikin Tsabta, amma ba sai kin bashi dama ya gan Jikin ki ba. Kiyi Kwalliya irin da Musulunci, kada ki saka turare mai Kwamshi sossai domin kuwa wannan kadai na iya saka mishi sha’awar ki.
Ummulkhairi Hayatuddeen
Allah sa mu dace.
MUJALLARMU

COMMENTS

Name

AL-AJABI,25,BIDIYO,1,BIRNIN-KEBBI,26,DUNIYA,23,FADAKARWA,23,FASAHA,3,HOTUNA,40,JAKAR MAGORI,18,LABARI,422,NISHADI,51,SANARWA,13,SHARHI,13,SIYASA,17,TARIHI,7,WASANNI,8,
ltr
item
ISYAKU.COM: Abubuwan da za ki yi yayin da kike soyayya da saurayin ki
Abubuwan da za ki yi yayin da kike soyayya da saurayin ki
https://3.bp.blogspot.com/-0ihUbVWT4tk/WIpP_xl4krI/AAAAAAAACP0/W-TB4Un4O5MWO25J1hQj7Y1V2ZwQ1AErQCLcB/s1600/LADY.jpg
https://3.bp.blogspot.com/-0ihUbVWT4tk/WIpP_xl4krI/AAAAAAAACP0/W-TB4Un4O5MWO25J1hQj7Y1V2ZwQ1AErQCLcB/s72-c/LADY.jpg
ISYAKU.COM
http://www.isyaku.com/2017/01/abubuwan-da-za-ki-yi-yayin-da-kike.html
http://www.isyaku.com/
http://www.isyaku.com/
http://www.isyaku.com/2017/01/abubuwan-da-za-ki-yi-yayin-da-kike.html
true
3052478943858316060
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts KARANTA SAURAN LABARAI Karanta saura Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All KARANTA WADANNAN LABEL MAADANI BINCIKA GABADAYAN LABARAI Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS CONTENT IS PREMIUM Please share to unlock Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy