• Labaran yau

  December 05, 2016

  ZA AYI FADAN KARSHE TSAKANIN SOJOJI DA ‘YAN BOKO HARAM-BURATAI

  Shugaban rundunar sojin Najeriya laftanar Janar Tukur Buratai, ya bukaci sojojin dake fafatawa da ‘yan Boko Haram a yankin Arewa maso gabas da suyi shirin fadan karshe da’ yan ta’addan,
  domin kuwa babu tsarin shiga Sabuwar shekarar 2017 ba tare da an gama da su ba.
  “Kodai mu samu nasarar karkade kurarsu da ta rage ko kuma mu cigaba da fafatawa ba kakkautawa, a cikin wannan halin kangin maras dadi na ta’addanci a yankin nan na Arewa maso gabas”.
  “yana mai fada da kakkausar murya ga rundunar sojojin, tare kuma da jaddada cewa watan Disamba (December) yadda yazo a watan karshe na shekara haka su ma ‘yan Boko Haram kasrshensu ya gabato”
  Buratai yayi alkawarin mayar da sojojin barikinsu a cikin shekarar da zamu shiga ta 2017. Janaral Buratai yayi alkawarin zuwa da kansa filin daga yayin da ake fafatawa da’ yan Boko Haram din.
  Yadai yabawa sojojin tare da nuna jin dadinsa a kan irin sadaukar da suke yi na kare kasarsu.
  A karshe kuma yayi kara ga duk jagororin bataliyoyin sojojin da su shirya kai hare-hare zafafa aka ‘yan Boko Haram din musamman sojojin sama.
  Daga Labarai24.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: ZA AYI FADAN KARSHE TSAKANIN SOJOJI DA ‘YAN BOKO HARAM-BURATAI Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama