YADDA ZA KA HANA SAKONNIN TALLA NA SMS SHIGOWA WAYAR KA DAGA MTN,AIRTEL GLO DA SAURAN SU

Hukumar sadarwa ta  NCC ta umarci kamfanonin samar da layin wayar salula na Najeriya da cewa dole ne su samar da hanyar da masu amfani da wayar salula zasu iya zaben irin tallace tallacen da su kamfanonin ke aikowa ga mai amfani da layim salular nasu.

Duk dan Najeriya dai shaida ne ga irin cin mutuncin da wadannan kafafen sadarwar wayar salular ke yi wa masu amfani da layukan su wajen aiko sakonnin da baka bukata.Ga yadda za ka yi ka hana irin wannan tallan shigowa wayar ka.
1.Ka je rumbun sakonnin wayar ka watau message.
2.Ka rubuata STOP 
3.Ka aika zuwa 2442 
Wannan zai baka zabin ko ka hana samun sakonnin talla gaba daya,ko ka zabi irin tallar da kake son kamfanin sadarwar ta dinga aiko maka.Wannan tsarin yana ammfani a kowane irin layin salula,ko MTN,AIRTEL ko GLO.

YADDA ZA KA HANA SAKONNIN TALLA NA SMS SHIGOWA WAYAR KA DAGA MTN,AIRTEL GLO DA SAURAN SU YADDA ZA KA HANA SAKONNIN TALLA NA SMS SHIGOWA WAYAR KA DAGA MTN,AIRTEL GLO DA SAURAN SU Reviewed by on December 10, 2016 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.