• Labaran yau

  December 02, 2016

  WANI KUREGE YA SAMI NASSARA KAN MACIJI  Fada tsakanin wani kurege a daji da maciji wanda ya kare ba yadda kuke tsammani ba. Tun muna yara kanana mun san cewa kurege halitta ce mai kyau wadda yawan ci mun san yana kwakulo gyada daga rami dan yaci
  kuma ba komai ya damu da shi ba, amma ina ga ba ko wanne kurege ne na kwarai. Wani kurege na nahiyar Afrika ya samu nasarar samun daukar kanun labarai bayan farmakin da ya kaima wani maciji a karan battar da yayi nasarar kashe maciji. Fadan ya nuna mana cewa jajirtaccen kuregen ya hau kan macijin kuma ya hana macijin yin motsi da wutsiyar sa.
  Kuregen ya kara dawowa in da ya kara danna hakoran shi a cikin jikin maciji, shi kuma ya ta kakarin kare kansa. Macijin yayi kokarin dago kanshi yayi tsargi duk dan ya samu ya kubuta da ga hannun kuregen amma abun ya faskara. Sai dai macijin yayi kokarin fasa kansa ya ture kuregen daga jikin sa. Jajirtaccen kurege yaki ya bada gari inda ya cigaba da cizon macijin shi kuma yayi ta kokarin ramawa. Daga karshe dai kurege yayi nasara in da ya bar macijin a kwance cikin jini.

  Daga Nasir Umar Bello naij.com

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: WANI KUREGE YA SAMI NASSARA KAN MACIJI Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama