NAJERIYA TA FITAR DA SABBIN SHARUDDAN AIKIN HAJJI

Hukumar kula da aikin hajji ta Najeriya ta fitar da wasu sabbin sharudda da ta ce dole ne, duk wani maniyyaci ya cika su kafin ba shi damar zuwa aikin hajji a Saudiya.
A cewar shugaban sashin hulda da kafafen yada labaran hukumar, Alhaji Uba Mana, sharudan za su taimaka wajen kawo karshen samun masu safarar miyagun kwayoyi da ke shiga cikin maniyatan Najeriya, da kuma aikata sauran laifuka a yayin aikin hajji.
Mana ya ce yanzu tilasne  maniyyaci ya gabatar da wani sahihin mutum, da zai tsaya masa kafin ba shi damar zuwa aikin hajji, wadanda suka hada da, limamin masallacin Juma’a da ma’aikacin gwamnati da ke mataki na 12, ko kuma mai mukamin sarautar gargajiya.
RFI HAUSA

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN