MATASHI YA KASHE MAHAIFIYAR SA A JIHAR OGUN

Akwai wani tashin hankali da jami’an yan sandan jihar Ogun suke fuskanta a yankin kudu maso yammacin Najeriya.
Sun damke wani Segun Ogunlusi wanda ya hallaka mahaifyarsa, Abimbola Ogunlusi,kuma ya birne ta a salga,
game da rahoton da jaridar Punch ta bayar na cewan wannan abu ya faru ne ranan Talata , 13 ga watan Disamba a Oketunde Street, Molatori, Ogijo,karamar hukumar Sagamu a jihar.
Kakakin hukumar yan sanda jihar, Abimbola Oyeyemi, ta tabbatar da cewa kanwar sa, Yetunde Ogunlusi,ta kai kara ofishin yan sanda.
Yan sandan sune Yetunde ta bayyana cewa mahaifyarsu ta bar gida lokacin da take zuwa aiki ranan Talata,13 ga wata Disamba,2016 kuma da ta dawo, bata ganta ba.
Oyeyemi tace:“Ta kara bayyana cewa lokacin da ta tambayi yayanta,Segun, wanda ke tare da mahaifiyar a gida, abin da ya fada mata bai gamsar da ita ba.
“Bias ga rahoto, shugaban yan sandan yankin Ogijo ,Ahmed Tijano,ya jagoranci yan snada zuwa gidan da ke Oketunde , Molatori, Ogijo, kuma aka damke shi.”
A lokacin binciken, yan sanda sun bayyana cewa Segun ta kashe mahaifiyarsa kuma ya birne ta a salgan da ke kusa da gidan.
Naij.com hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN