• Labaran yau

  December 06, 2016

  KIRISTA SUN LASHI TAKOBIN KAI WA MUSULMI HARI A KADUNA


  Akwai tashin hankali a jihar Kaduna,yayinda matasan addinin kirista sun sha alwashin zasu kai kari duk lokacin da Fulani makiyaya suka sake kawo musu hari a kudancin jihar Kaduna.

  Jaridar Punch ta bada rahoton cewa Matasan suna wannan barazanar ne bayan sun gano wani munafurci a bangaren jami’an tsaro.
  Game da cewarsu, tunda gwamnan jihar Nasir El- Rufaí yace Fulanin da ke kai musu hari bay an Kaduna bane,toh gwamnatin tarayya ta kulle iyakokin kasar Chadi, Kamaru da Benin.
  Kana sunyi kiraga majalisar dokokin jihar Kaduna su tsige Gwamna El-Rufai da gaggawa saboda laifin hada baki da yan taádda su kasha yan Najeriya.
  Matasan masu Magana karkashin jagorancin Kungiyar Kiristocin Najeriya , sun soki shirin gwamnan na baiwa Fulani makiyaya kudi akan awakinsu da suka bace,kuma sun soki maganar da yayi akan shugaban Kungiyar C.A.N, Dr Samson Ayokunle.
  Shugaban Matasan yace: “Ko Fulanin yan Najeriya ko yan kasan waje ne, mu matasan Kirista mun yi ittifakin cewa wannan yunkurin kasha kiristoci ne a Najeriya. Saboda haka, muna kira ga Kirista su dau makami.
  Mudathir Ishaq naij.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: KIRISTA SUN LASHI TAKOBIN KAI WA MUSULMI HARI A KADUNA Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama