HANKALIN PAPAROMA YA TASHI SAKAMAKON GANO WANI BIBLE INDA "JESUS" YAKE WASIYYAR ZUWAN ANNABI MUHAMMAD (S.A.W)

'Yan sanda a kasar Turkiyya sun gano wani tsohon littafin bible wanda ake kyautata zaton a cikinsa akwai inda, Annabi Isah A.S (Jesus) ya yi wa mabiyansa albishir da zuwan Annabin karshe mai suna Muhammad (Annabi Muhammadu S.A.W).
An yi ittifakin cewa Littafin ya kai shekara 1,500 da rubutawa. Kuma an rubuta shi ne da ruwan zinari a cikin harshen "Aramaic" (Larabci).
Jaridar Daily Mail ta Amerika ta ruwaito cewa, gano littafin wanda aka yi hasashen duk falle daya a cikinsa zai kai kimanin Yuro milyan £14 ya jawo muhawara mai tsanani a tsakanin mabiya darikar Vatican da musulmi inda har Fafaroma Pope Benedict XVI ya nemi a kawo masa bibile din ya gani.
Idan dai aka tabbatar da zargin da ake yi akan Bible din kuma ta tabbata haka din ne. To akwai chakwakiya ganin cewa littafin zai karyata mabiya addinin kirista dake Allantar da Isah (AS) da kuma masu cewa Jesus din dan Allah ne.  Bible din zai tabbatar da cewa addinin Islama shine gaskiya kuma Musulmai sune ke kan addini na gaskiya wanda (Almasihu/Jesus) ya umurci mabiyansa akai.
Majiyar ta mu ta kuma ruwaito cewa an gano littafin ne tun a shekara ta 2000 amma hukumomin kasar Turkiyya suka cigaba da tsaron shi har zuwa shekara ta 2012 inda suka kaishi gidan tarihi na Ankara Ethnography Museum. Kuma ana sa ran nan bada jimawa ba za'a rika nunawa mutane Bible din a gidan tarihin kasar.
Ministan raya Al'adu da yawon bude ido na kasar Turkiyya, Ertugrul Gunay ya ce suna kyautata zaton Bible din na gaskiya ne shi yasa wasu suka boye shi saboda yadda littafin ya yi bayani akan ainihin matsyin Almasihu (Jesus) sabanin tunaninsu.
Jaridar ta daily mail ta kara da cewa hankalin fafaroma da sauran manyan limaman kiristoci ya tashi sakamakon gano wannan littafi na Bible.
DAGA HAUSA TIMES

Gida - Leadership Hausa

Assalamu alaikum, Editan LEADERSHIP Hausa mai farin jini, ka bani dama na yi kira ga gwamna Kashim...

Gida

(null)

Labarai, kai tsaye- Radio France Internationale RFI

Samu dukkanin shirye-shiryen RFI Siyasa da Al'adu da Wasanni da Labarai da dumi-duminsu na Afrika da Faransa da duniya.

NIGERIAN NEWSPAPERS

Flash or unlock your phone at SENIORA TECH shop No.51 upstairs.OLUMBO shopping complex Ahmadu Bello way Birnin kebbi. 08062543120 http://...

Wasanni

Domin samun labaran wasanni kai tsaye daga club na kwallon kafa na turai

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN