GWAMNATIN NAJERIYA TA HANA SHIGOWA DA MOTOCI TA KASA

Gwamantin Najeriya ta ce za a hana shigowa da motoci ta kasa daga farkon watan Janairu mai zuwa a duk fadin kasar.
Wata sanarwa da hukumar hana fasa kauri wato Kwastam ta fitar, ta bayyana cewa, hanin ya shafi sabbi da tsoffin motoci.
Babbar manufar gwamnatin ta Najeriya ita ce, tabbatar da cewa dukkanin motocin da za a shigo da su a kasar, ya kasance ta tashoshin ruwa ne kawai. kamar dai yadda ta dauki irin wannan mataki akan masu shigo da shinkafa a kasar.
RFI Hausa
GWAMNATIN NAJERIYA TA HANA SHIGOWA DA MOTOCI TA KASA GWAMNATIN NAJERIYA TA HANA SHIGOWA DA MOTOCI TA KASA Reviewed by on December 09, 2016 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.