FASINJOJI 92 DA KE JIRGIN YAKIN RASHA SUN SALWANTA A TEKU

Ma’aikatar tsaron kasar Rasha ta ce jirgin yakinta mai dauke da fasinjoji 92 da ta sanar da bacewarsa, ya afka cikin tekun Bahar Maliya...

Ma’aikatar tsaron kasar Rasha ta ce jirgin yakinta mai dauke da fasinjoji 92 da ta sanar da bacewarsa, ya afka cikin tekun Bahar Maliya.
Rahotanni sun ce jirgin yakin ya bace ne bayan kimanin mintuna 20 da tashinsa daga yankin So
chi da ke kasar Rasha, da nufin zuwa birnin Latakia da ke Syria.
Wata tawagar jami’an ceto ce ta tabbatar da hadarin jirgin, bayan gano wasu daga cikin baraguzansa a gabar tekun da ke kusa da birnin na Sochi.
Ma’aikatar tsaron Rasha ta ce jirgin yakin, kirar Tu-154 yana dauke ne da Jami’an kasar da suka kware wajen, kidan goge irin nasu daga sananniyar kungiyar da ta yi fice kan hakan wurin bukukuwa a kasar, mai suna ‘Alexandrov Ensemble, da kuma wasu ‘yan jaridu guda 9 sai kuma ma’aikatan jirgin guda 8, lokacin da jirgin yayi hadari.
Bainciken da jami’an Rasha suka gudanar ya nuna cewa ba rashin kyawun yanayi bane ya haifar da hadarin jirgin, lamarin da yasa suka zurfafa binciko dalilin faduwarsa.
Jirgin yakin dai hasali ya taso ne daga babban birnin kasar Moscow, inda ya sauka a fillin jiragen sama na Sochi tare da kara mai, inda ya kuma tashi zuwa birnin Latakia da ke Syria.
Har yanzu dai babu fasinja guda da rayu, da aka samu nasarar ganowa.
RFI HAUSA Saurari RFI Hausa

COMMENTS

VISITOR
Name

AL-AJABI,22,BIRNIN-KEBBI,21,DUNIYA,19,FADAKARWA,22,FASAHA,3,HOTUNA,34,LABARI,351,NISHADI,49,SANARWA,13,SHARHI,8,SIYASA,15,TARIHI,7,WASANNI,8,
ltr
item
ISYAKU.COM: FASINJOJI 92 DA KE JIRGIN YAKIN RASHA SUN SALWANTA A TEKU
FASINJOJI 92 DA KE JIRGIN YAKIN RASHA SUN SALWANTA A TEKU
https://3.bp.blogspot.com/-1G-KPWxnhAw/WGAGw553i3I/AAAAAAAABVA/tXJOnCpw9iYFNtNQKW203IE0bbkoQHvogCLcB/s320/tu154chelyabinsk.jpg
https://3.bp.blogspot.com/-1G-KPWxnhAw/WGAGw553i3I/AAAAAAAABVA/tXJOnCpw9iYFNtNQKW203IE0bbkoQHvogCLcB/s72-c/tu154chelyabinsk.jpg
ISYAKU.COM
http://www.isyaku.com/2016/12/fasinjoji-92-da-ke-jirgin-yakin-rasha.html
http://www.isyaku.com/
http://www.isyaku.com/
http://www.isyaku.com/2016/12/fasinjoji-92-da-ke-jirgin-yakin-rasha.html
true
3052478943858316060
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All WASU KARIN LABARAI LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS CONTENT IS PREMIUM Please share to unlock Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy