AN KAMA BATAGARIN JAMI'AN TSARO DA KE YI WA MATA FYADE

Kamfanin dillancin labarai (NAN) ta ruwaito cewar an kama yansanda guda 2, Sojoji 4, ganduroba 1, jami’i a ma’aikatan kula da harkokin noma na jihar Borno da jami’an rundunar sa kais u 2 da laifin cin zarafin mata da yan mata wadanda rikicin Boko
Haram ya sabauta, ta hanyar tursasa saduwa dasu a sansanin yan gudun hijira.
Yayin da yake jawabi a ranar Talata 6 ga watan Disamba, babban hafsan yansanda Ibrahim Idris yace zasu cigaba da hada kai da sauran hukumomin tsaro, musamamn wadanda abin ya shafa don su tabbatar da sun miko jami’an nasu da ake zargi, don gudanar da bincike.
Idris yace da zarar an kammala bincike, duk wanda aka kama da laifi a cikinsu, zai dandana kudarsa, sa’anan zasu sallame shi, sa’anan zasu mika shi gaban kotu.
I.G Ibrahim yace, “zamu gudanar da bincike na gaskiya, kuma duk wanda muka kama da laifi zamu sallame shi, daga nan sai mu kais hi kotu.
Bincike da ake yi ya biyo bayan umarni da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baiwa I.G Idris sakamakon wani rahoton da kungiyar kare hakkin dan Adam ta fitar a watan Oktba inda tayi zargin wasu jami’an gwamnati na cin zarafin yan mata da kananan yara a sansanonin yan gudun hijira dake jihar Borno.
Da wannan ne ya sanya rundunar yansanda kafa kwamitin bincike don tabbatar da sahihancin zargin tare da kama masu laifin.
Naij.com
AN KAMA BATAGARIN JAMI'AN TSARO DA KE YI WA MATA FYADE AN KAMA BATAGARIN JAMI'AN TSARO DA KE YI WA MATA FYADE Reviewed by on December 08, 2016 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.