ABUBUWA 4 DA MACE ZA TA YI IN AKA YI MATA FYADE

images-3

Sakamakon yawaitar karuwar yiwa mata fyade da maza ke yiwa mata a Najeriya da ma duniya baki daya, ya zama lallai mata su san abubuwan da ya kamata su yi idan a kayi rashin sa’a ta gamu da ‘yan daukar amarya ko kuma wata’ yar uwarta mace aka yi mata fyade,
to menene abinda ya kamata su fara yi?
Fyade na janyo wata babbar damuwa ga gangar jiki da kuma dabi’ar wanda aka yiwa fyaden ta hanyar damuwa da bakin ciki da tashin hankali da kuma zurfaffen tunanin da ba na lafiya ba.
Amma fa abinda ya kamata wadanda aka yi wa fyaden su gane shi ne yawanci ba laifinsu bane, saboda haka kar ki dorawa kanki laifi ki na zargin kanki, maza karki kasa a gwuiwa wajen neman magani da kuma shawarwarin likita.
Saboda haka ga wasu abubuwa 4 da ya kamata kowacce mace ta sani domin daukar matakin gaggawa a duk sanda aka samu faruwar wannan TA’ADDANCI a gare ta ko wata ‘yar uwarta mace.
1- GARZAYA KI NEMI MAFAKA
Abu na farko da ya makata ki yi shi ne ki bar wurin da aka yi miki wannan ta’annati izuwa wurin da kika yarda kika amince da shi nesa da inda abin ya faru. Walau gidan ‘yan uwanki ko kuma gidan aminiyarki. Kada ki tsorata domin har yanzu kina raye kuma ba kanki farau ba, a saboda haka kar ki ji kunya domin fyade ne aka yi miki ba Zina kika yi ba, saboda haka karki ji kunyar tattaunawa da wanda kika amince da shi sosai domin yin hakan zai taimaka wajen yarda da aminci a zuciyarki da kuma wanda kika fadawa domin ya samu kwarin gwuiwar baki shawarwari da kuma tausarki.
Akwai kungiyoyi masu zaman kansu wadanda suke yaki da kuma kwato ‘yanci gami da tabbatar da adalci ga duk wacce aka yi wa wannan aika-aika, kuma suna da kwararru da za’ a su baki shawarwari a kan lafiyar ki. images-2
2- GARZAYA ASIBITI DOMIN GWAJI
A asibiti ne kadai zaki samu cikakkiyar kulawar kwararrun likitocin da suka kware a fannin maganin jima’i wadanda za su auna ki domin fitar da rahotan da zai nuna zurfi da kuma irin illar da kuma matakin fyaden wanda zai taimakawa ‘yan sanda wajen bincike da kuma shaida a kotu.
Za’ a yi miki gwajin cuta mai karya garkuwar jiki (HIV) da kuma sauran cututtukan da ake dauka yayin jima’i (STD) da kuma gwajin juna biyu (Ciki) Tare da baki maganin daukar cikin, domin kuwa shi la’anannen maras imanin da yayi fyaden watakila yana dauke da cututtukan da sai an gwada za’a gani. ‘Yar uwa kada ki boye ko kiji tsoro ballantana kunya domin in kinki zuwa dayan abubuwan da muka fada na iya faruwa da ke.
A shawarce kada kiyi wanka, kada ki canja kanyan jikinki, kada ki goge ko wanke farjinki ballantana ki sha kowanne irin magani, za’a baki inda bukatar hakan a asibiti. images-4
3- SHIGAR DA RAHOTO WURIN ‘YAN SANDA 
Fyade babban laifi ne a dokar kasa wanda bai kamata wanda yayi ya tafi a banza ba, ba tare da an hukunta shi ba, don haka kada ki boye ta hanyar yin shiru, saboda haka maza ki garzaya domin shigar da rahotan faruwar lamarin ga hukumar’ yan sanda domin bi miki hakkinki,  tabbata kin basu cikkken labarin yadda abin ya afku domin su dauki jawabinki a rubuce wannan zai taimaka mutuka gaya wajen bibo miki hakkinki.
4- NEMI SHAWARWARI 
Fyade tun daga kalmar ma ba abu ne mai dadi ba, a saboda haka duk wanda aka yi wa na iya fuskantar matsalar damuwa da zurfaffen tunani wanda zai iya janyo mata doguwar matsala. Wasu da aka yi wa fyade na iya cintar kansu a mummunan halin bakin ciki gami da kunci (PTDS) tare da tsanar mutane musamman maza wanda wannan na iya shafar yadda za suke tunani da kuma tafiyar da rayuwarsu, wannan dalili ne yasa suke da bukatar shawarwarin kwararrun masana.
Ya ‘yar uwa ki yi hakuri, ki zamto mai karfin gwuiwa da kuma jajircewa wajen bin hakkinki, ki dauka tamkar jarrabawa ce daga Allah kuma ki nemi taimakonsa. Kada ki yi shiru wannan TA’ADDANCI ya tafi a banza, ke kadai ce zaki iya fadar abinda ya faru a saboda haka kada kiyi kasa a gwuiwa ballantana ki ji tsoro ko kunya. 
Daga Abubakar SD.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN