ZAMFARA: AN KASHE MUTANE 40 A WATA MAHAKAR ZINARI


Rahotanni daga jihar Zamfara sun ce kusan mutane arba'in ne aka kashe a cikin wani hari da wasu 'yan bindiga suka kai kan wata mahakar Zinari.
Haka ma wasu mutane da dama sun bata yayin da wasu suka tsira da munanan raunukka a cikin harin da aka kai ranar Litinin kan mahakar zinarin wadda ke daura da kauyen Bindim na karamar hukumar Maru.
Mazauna yankin sun shaida wa BBC cewa harin ya zo bayan da 'yan bindigar wadanda ake zaton 'yan fashin shanu ne suka kwashe makonni suna satar mutane don neman kudin fansa.
''Yawancin wadanda suka mutun lebarori ne masu aikin hakar zinari da kuma wadanda suka zo saye.'' In ji wani mazauni yankin, kodayake kawo yanzu hukumomin tsaro a jihar ba su tabbatar da faruwar lamarin ba.
(Daga BBCHausa)

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN