• Labaran yau

  November 29, 2016

  RECTOR NA RIKON KWARYA NA FEDERAL POLYTECHNIC BAYELSA YA MUTU BAYAN YA WASKE WATA YARINYA

  Rector na rikon kwarya na Federal polytechnic Ekowe,na jihar Bayelsa ya yanke jiki ya fadi a dakin Hotel bayan ya gama shakatawa da wata yarinya da har yanzu ba'a gane ko wacece ba.Al'amari ya faru a Hotal din mai suna
  Zekoh Place a titin Onoharigho a Ughelli.An garzaya da shi zuwa wani Assibiti mafi kusa da Hotal din inda Likita ya tabbatar da mutuwar sa.

  SHARHI

  Me ke kawo irin wannan mutuwar gaggawa?...wani dan binciken da nayi ya nuna cewa:
  1.Ciwon zuciya-wanda zai iya haifar da irin wannan mutuwar gaggawa,saboda a yayin jima'i aikin zuciya na karuwa da kusan kashi 15 zuwa 30 wanda ya banbanta daga wannan zuwa wancan.A yayin da zuciya ta dau aiki sosai ta hanyar al'amarin jima'i takan harba ta hanyar bugawa da wuri,bayan maniyi ya fita kuma sai bugun zuciyar ya dinga ragewa har ya koma daidai.To ga wasu mutane,yayin da zuciyar ta dinga bugawa da wuri kafin maniyi ya fito,ita zuciyar sai ta ci gaba da bugawa da wurwuri har ta zarce iya ka'idar da zuciyar zata iya bugawa wanda zai harfar da gazawar zuciya,watau HEARTH ATTACK.
  2.Ulcer ko gyambon ciki-Ulcer ko gyambon ciki yakan iya haifar da mutuwar gaggawa bayan ko yayin da ake jima;i,wannan ya danganta daga abincin da mutum ya ci lokaci kadan kafin ya fara jima'i.Saboda idan abincin da yaci yana haifar da hauhawan sinadarin acid na hydrochloric,wannan zai iya jawo bugawar zuciya da wuri har ya zarce ka'idar karfin jurewan da zuciyar zata iya yi wajen bugawa,daga bisani kuma sai ta tsaya wanda ke haifar da gazawar zuciya watau HEARTH ATTACK.
  3.Athsma ko Asma-Athsma,asma zai iya tasowa a dalilin cewa idan yarinyar da ta shigo daki ta shafa wani turare da zai iya zaburar da athsma a dalilin cewa kafin a sadu tsakanin na miji da mace,ai sai an rufe daki,hakan yana haifar da karancin iskar OXYGEN wanda zai iya sanadin gazawar zuciya wanda zai iya kai ga rasa rai.
  Allah ya kiyaye ya sa muyi kyakyawar karshe,Amin.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: RECTOR NA RIKON KWARYA NA FEDERAL POLYTECHNIC BAYELSA YA MUTU BAYAN YA WASKE WATA YARINYA Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama