• Labaran yau

  November 10, 2016

  KONGA TA BUDA SABON OFISHI A BIRNIN KEBBI DON BAYAR DA KAYAKIN DA AKA SAYE TA INTANET

  SADIQ ABUBAKAR NORTHWESTERN ZONE MANAGER
  Kamfanin sayar da kayaki ta intanet wanda ke kawo kayakin kai tsaye har gidan ka bayan ka saye daga intanet ta buda wani ofishin ta a  NO.12 Taushi Plaza yamma da gidan Wazirin  Gwandu.
  YANDA ZAKA SAYI KAYA A KONGA TA INTANET

  Da farko dai zaka iya shiga shifin nasu na konga.com sai ka danna alamar ragista,zai kai ka tsarin ragista kyauta,bayan haka sai ka nemi hajar da kake bukata,idan ka gan abin da kake so tau sai ka danna inda zai kai ka tsarin sayen wannan hajar.Za ka iya biyan kudin kayan da katin ka na banki watau mastercard ko visacard,ko kuma ka biya tsabar kudin bayan an kawo maka kayan a nan Birnin kebbi.
  RAPHAEL DA AKILU

  AMFANI DA WAYAR SALULA DON SAYEN KAYA A KONGA

  Za ka iya amfani da wayar salular ka don sayen duk abin da kake so a konga.com ba dole sai da na'urar komputa ba duk tsarin da za ka yi ammfani da shi domin mu'amala da konga da komputa zaka iya amfani da wayar salular ka don yin wannan cefanen.
  ZA KA IYA MAYAR DA KAYAN DA KA SAYE A KONGA IDAN DA MATSALA

  Bayan an kawo maka kayan da ka saye a konga sai aka gano akwai matsala da wannan kayan,zaka iya maidowa domin a musanya maka,bayan an bi wasu matakai masu sauki.
  .


  • Facebook Comments
  Item Reviewed: KONGA TA BUDA SABON OFISHI A BIRNIN KEBBI DON BAYAR DA KAYAKIN DA AKA SAYE TA INTANET Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama