• Labaran yau

  November 03, 2016

  FARASHIN ADAM A ZANGO A FIM YA KOMA NAIRA MILIYAN A DUK FIM DA ZAI FITO.

  Shahararren Jarumi, Mawaki, Mai bada Umarni, Mai koyar da rawa kuma mai Kamfanin shirya fina-finan Hausa Wato Adam A. Zango Ya Kara Farashinsa Da Yake Karba daga Naira Dubu Dari Shida (N600,000.00) Zuwa Naira Miliyan Daya (N1,000,000.00) a kowa fim da zai fito daga kashi na Daya zuwa kashi na hudu (1 to 4), haka kuma duk fim din da zai fito a a ciki in dai kashi daya zuwa biyu (1 and 2) zai amshi naira Dubu dari Biyar (N500,000.00). Majiyar Tamu ta Shaida mana Jarumin yayi wannan karin ne domin ya samu hutu kuma a kara samun Bulbulowar Sabbin Fuska duk da a yanzu haka an fara samun wasu Sabbin Jarumai Maza dake Motsawa a Masana'antar, Majiyar ya kara Shaida mana a yanzu haka babu wani Gurbi koda na kwana Biyu ne da Jarumin zai samu hutu indai ba inda ya ware dan hutu bane, dan koda wani Gyaran aikinsa nakan sane sai dai ya jira zuwa Ranan Hutun ko kuma sai wani Shekarar a cewar Majiyar Tamu.

  Wani na Hannun Damarsa ya sanar damu kamar haka "A ranar Asabar 4 ga Watan Yuni na wannan Shekaran 2016 ne Gidan Talabijin na DITV dake Jahar Kaduna Zasuyi Hira da mai Gidan mu Adam A Zango wanda Masoyansa da dama sun dade basuji duriyarsa ba a Kafafen Yada Labarai, sai kwatsam wani mai gabatar da shirin Mushakata a Gidan Talabijin din wato Gabiya ya kira Adam Zango a cikin shirin sannan yayi Alkawarin zuwa Yau din, amman kaga bai samu zuwa ba saboda yar Gajeruwa Rashin Lafiya dayi fama dashi" kaga tsabar rashin samun hutu ne ke kawo hakan, a gaskiya ni wani lokacin wallahi har tausayi yake bani don irin aikatuwar da yake yi, sannan kaga kuma wani dadin da dawar da zai baka tausayi yadda sauran yan fim zasu fito su sakata su wala shi baya iyawa domin duk inda ya bi Jama'a basu barinshi amman kasan kaunace ta kawo hakan, to kaga sai dai daga gida sai ofis dinsa ko gun aiki.
  Da muka leka dan kai tamu ziyarar da mai fatan kara samum lafiya dan gane da rashin lafiyar da kafan Talabijin din DITV tayi na baida lafiya an kara mai Ruwa, bayan jajanta mai da mai fatan Alheri, sai ya baiyana mana ciwon tapot ne ya dan kwantar dashi amman yanzu Alhamdulillah ya samu sauki, sannan kuma yayi Godiya ga Masoyansa da Addu'o'i dasuke masa wanda yake matukar bukata daga garesu yana Godiya matuka, dafatan Allah yabar zumunci.

  (Daga Kannywoodtoday)
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: FARASHIN ADAM A ZANGO A FIM YA KOMA NAIRA MILIYAN A DUK FIM DA ZAI FITO. Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama