• Labaran yau

  November 11, 2016

  BUTULCI KO RASHIN HAKURI DA RAGOWA ?

  A jiya Alhamis 10/11/16 ne da misalin karfe shida da rabi na yamma wani mai gyaran waya a garin Bunza ta jihar Kebbi mai suna Abubakar Idris ya kai karan wani Aminu shi ma mai flashin na wayoyi a Olumbo plaza da ke kan titin Ahmadu Bello da ke Birnin kebbi.
  Shi dai Abubakar daraktan Seniora Tech,wanda shine ya taimake shi da wani bangaren ilimin na gyaran waya kuma mai gida ga shi Abubakar din da Aminu ya yi yunkurin yin sulhu a tsakanin su domin rigimar akan naira dubu goma sha takwas ne.Sai shi uban gidan nasu ya bukaci Abubakar ya dawo ranar Laraba 8/11/16 domin ya karbi kudin sa N18000,Abubakar bai zo ba kuma bai aiko da sako ba kuma ba kiran wayan salula ko bayani kan rashin zuwan nashi,kwastsam ranar Alhamis 10/11/16 da karfe shida da rabi na magariba sai ga Abubakar ya bullo.Da aka yi masa bayanin cewa ai an ajiye mashi kudin sa ranar Laraba amma bai zo ba kuma aka ci gaba da ajiyan kudin har Alhamis zuwa karfe shida kuma bai zo ba sai aka yi amfani da N15000 daga cikin kudin amma don Allah ranar Juma'a da la'asar ya zo ya karbi kudin sa gaba daya watau N18000 amma Abubakar ya ki,duk jama'an da ke nan sun bukaci ya yi hakuri ya zo ranar Juma'a amma ya ki,sai ya je ya gayyato jami'an tsaro na CIVIL DEFENCE inda aka je can ofishin su aka yi sulhu,a dole dai sai ranar Juma'an bayan la'asar watau karfe 4:00pm,kuma har an riga an kai kudin tun karfe 1:15pm.
  Wannan yana nuni da duk mai gyara idan dai gyara ne na hannu,tau da bukatar ka yi ingattaccen nazari kafin ka yi tunanin koya wa wani aiki,saboda butulci,cin amana,rashin ragowa shi ne adon zamani musamman ga wanda ya kwashi ilimin da bai wahala ba balle ya san mahimmancin guzurin rayuwan da Allah ya kaddari ka bashi.Irin wa'yannan mutanen ka bar su kawai da halin su,domin zaka ga babu wani ci gaba illa asara,wahala da koma baya a cikin sha'anin su.  • Facebook Comments
  Item Reviewed: BUTULCI KO RASHIN HAKURI DA RAGOWA ? Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama