• Labaran yau

  November 15, 2016

  BOKO HARAM TA SAKE KASHE WANI BABBAN SOJAN NAJERIYA

  Rahotanni sun nuna cewa Boko haram ta sake kashe wani babban sojin Najeriya Laftana kanar mai kula
  da bataliya ta 114 ta dakarun musamman ya hadu da ajalin sa ne yayin wani kwanton bauna da 'yan boko haram din suka yi ranar Litinin 14/11/2016 da safe inda suka  halaka shi tsakanin Bita da Piridang.

  Jaridar Premium times ta ruwaito cewa,motar da kwamandan ke ciki ne ya taka wata nakiya da aka bi
  nne a gefen titi,bayan fashewar nakiyar kwamandan bai raunata ba amma lokacin da ya fito daga motar don ya duba barnar da nakiyar tayi sai 'yan boko haram din suka buda masa wuta da bindigogi.

  Sojojin dai ance suna kan hanyar su ce ta zuwa Yola ta jihar Adamawa daga Bita ta jihar Barno,hukumar sojin Najeriya dai ta bakin kakakin ta, ta ce bata da masaniya game da wannan al'amari ko mutuwar laftana kanar Umar.

  (Daga naij.com)
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: BOKO HARAM TA SAKE KASHE WANI BABBAN SOJAN NAJERIYA Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama