BOKO HARAM TA KASHE WANI BABBAN SOJIN NAJERIYA

Marigayi Laftanar Kanar Muhammad Abu Ali lokacin da ake masa karin girma
Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da mutuwar Laftanar Kanar Muhammad Abu Ali, tare da wasu sojojin hudu, lokacin da suka dakile wani harin mayakan Boko Haram a kan barikin sojin kasar na 119 dake Mallam Fatori, jihar Borno.
Laftanar Kanar Muhammad Abu Ali, shi ne kwamandan runduna ta 272 mai kula da tankokin yaki.
Cikin wata sanarwa, kakakin rundunar sojin kasar, Kanar Sani Uman Kukasheka, ya ce sojojin sun kashe mayakan Boko Haram din goma sha hudu a lokacin arangama tare da kwace makamai da dama.
A shekarar 2015 aka yiwa Laftanar Kanar Muhammad Abu Ali, karin girIma daga Manjo zuwa Laftanar janar saboda jarumtakan daya nuna a Gamboru Ngala.
(Daga RFI Hausa)
BOKO HARAM TA KASHE WANI BABBAN SOJIN NAJERIYA BOKO HARAM TA KASHE WANI BABBAN SOJIN NAJERIYA Reviewed by on November 06, 2016 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.