• Labaran yau

  October 26, 2016

  SOYAYYAR ADAM ZANGO DA ZAHRA BUHARI

   
   A yan kwanakin nan wata jitajita kan shahararran Mawaki kuma Jarumi Adam A. Zango da diyar shugaban Kasan Najeriya Zahra Buhari ke yaduwa a shafin yanar gizo na sada zumunta ke ta bazuwa akan soyayya na tsakaninsu, ganin wani hoto da jarumin yasa a shafinsa na sada zumuntar facebook da Instagram wanda suke tare da 'yar shugaban Kasa Muhammad Buhari yasa wasu keta baza jita jiar cewa suna soyayyane.

  Dan ganin hakan yasa wakilinmu a Jahar Kaduna baiyi wata wata ba inda ya nemi jarumin ta wayarsa inda bai sameshiba sai yayi tattaki zuwa ofishinsa dake Dandalin Murtala Square a Kaduna, da zuwansa kuwa yayi arba da Jarumin sannan ya tambayeshi shin ko ya gaskiyar batun soyayyarsa da diyar shugaban Kasa Muhammad Buhari Zahra, sai yace " Uhmm abin sirri ne" sai kuma yayi gum bai kara cewa komai da wakilin namu ya kara matsala lamba akan wasu zasu so sanin sirrin dake tattatare da batun sai yace "Magana ta tafarko dai itace Abin sirri ne". To me zakace ga masoyanka "Ina masu fatan Alheri sannan a ranan Juma'ar nan zan sako masu fim din Ramlah wanda nasan suna nan suna jiranshi".

  Tun dai ranan Talatar nan ne da jarumin ya sanya hotonsa da Zahra Buhari wannan Jita jitar ya bazu.
  Labari daga kannywoodtoday.


  • Facebook Comments
  Item Reviewed: SOYAYYAR ADAM ZANGO DA ZAHRA BUHARI Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama