• Labaran yau

  October 22, 2016

  Rikicin Masallacin Sultan Bello Kaduna: Da Sauran Rina A Kaba  Rikicin Masallacin Sultan Bello Kaduna: Da Sauran Rina A Kaba

  – Ba Mu Amince Da Nada Dakta Khalid Ba —Shaikh Ahmed Gumi
  – Riko Aka Ba Shi —Shaikh Baban Tune
  Tun bayan dakatarwar da aka yi wa limamin masallacin Sultan Bello da ke Unguwar Sarki Kaduna, Shaikh Balale Wali, kawunan malaman da ke da hannu a sha’anin Masallacin ya rabu wurin nada wanda zai ci gaba da limanci.
  Shaikh Ahmad Mahmud Gumi da wasu da suka kira kansu da almajiran Shaikh Abubakar Gumi sun fitar da sanarwar cewa ba su yadda da nada Babban Sakataren Jama’atul Nasrul Islam, Dakta Khalid Abubakar Aliyu a matsayin sabon limamin masallacin ba. Sun bayyana cewa hanyoyin da aka bi wajen zaben sa sun saba wa koyarwar Alkur’ani da Sunna.
  Sun ci gaba da cewa ba a tuntubi wadanda ya kamata ba kafin nadin. Sannan ana yunkurin karya tsarin da Shaikh Abubakar Gumi ya kawo a masallacin. Kuma an yi hakan ne don a haifar da rikici a masallacin.
  Shaikh Ahmad ya zargi Dakta Khalid da cewa yana kulla makirci don ganin ya sami wannan limancin ta hanyar zuga wasu daga cikin ‘yan kwamitin masallacin don su kawo tarnaki ga koyarwar Malam. Daga nan ya kuma bayyana cewa Dakta Khalid Abubakar ba dan makarantar Shaikh Abubakar Gumi ba ne.
  Shaikh Ahmad Mahmud Gumi ya roki mutanen da ke Sallah a Masallacin da kada su dauki doka a hannunsu saboda a cewarsa maganar tana hannun hukuma.
  A nashi martanin, shugaban Majalisar Limamai da Ladanai ta Jihar Kaduna, Shaikh Usman Abubakar Baban Tune, ya musanta nadin Dakta Khalid Abubakar Aliyu a matsayin Limamin Masallacin tare da nunar da cewa riko aka ba shi kafin a warware matsalar da ake fama da ita.
  Baban Tune ya ce ba su ji dadin abin da ya faru a masallacin na Sultan Bello ba kuma tuni suka bayyana wa Limamin Masallacin, Shaikh Balele Wali rashin hakurin da ya nuna kana suka tabbatar wa Shaikh Ahmad Mahmud Gumi cewa bai yi laifi ba da ya jagoranci Sallar Idi a ranar Babbar Sallah.
  Ya kuma bayyana cewa Masallacin Sultan Bello yana karkashin kulawar Mai Martaba Sarkin Zazzau ne da kuma Mai Alfarma Sarkin Musulmi, don haka su suke da ikon cire Liman da kuma nada wani.
  Ya nunar da cewa laifin da Liman Balele Wali ya aikata, ba daidai ba ne. Amma tuni ya rubutar takardar ba da hakuri. Don haka ya ce ba a sauke Shaikh Balele Wali ba har sai Sarkin Zazzau ko Sarkin Musulmi ya sanar da cire shi.
  Baban Tune ya jaddada cewa ba zai yiwu a bar masallacin ba tare da jagoranci ba, shi ya sa aka nada Dakta Khalid Abubakar a matsayin wanda zai kula da Masallacin har zuwa lokacin da za a warware matsalar da ake ciki.
  Ya bayyana Dakta Khalid Abubakar Aliyu a matsayin wanda ya cancanta da wannan riko musamman kasancewarsa daya daga cikin wadanda suke ba da karatu a wannan Masallaci.
  Daga Leadership Hausa
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Rikicin Masallacin Sultan Bello Kaduna: Da Sauran Rina A Kaba Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama