Rashin kudi ya haifar da takaitar hada hada a kasuwar wayan salula a Birnin kebbi

Olumbo plaza Birnin kebbi  
  Yanayin rashin kudi ya haifar da takaitar hada hada da aka sani a kasuwar hada hadan harkar wayar salula da sauran kayakin wayar a Olumbo plaza wanda ke yamma da gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello da ke garin Birnin Kebbi a jihar Kebbi.
 Wannan wurin dai ya shahara sosai kan harkar gyaran wayar salula,sayar da sababbi da kuma wayar salula da aka shigo da su daga Turai ko kasar Ingila da aka fi sani da London use ko tokumbo.Mafi yawan masu shagunan na zaune,zaman jiran kostoma wayanda ke shigowa daya bayan daya sabanin da inda zaka sami cincirindon kostoma musamman a shagunan masu gyaran wayar.Allah ya kawo alkhairi amin.
Rashin kudi ya haifar da takaitar hada hada a kasuwar wayan salula a Birnin kebbi Rashin kudi ya haifar da takaitar hada hada a kasuwar wayan salula a Birnin kebbi Reviewed by Isyaku Garba on October 17, 2016 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

Powered by Blogger.