• Labaran yau

  October 31, 2016

  RAHAMA SADAU TA DIRA AMERICA

  Shararriyar jarumar fina-finan Hausa Rahama Sadau daga Najeriya ta isa kasar Amerika domin gudanar da aikin hadinguiwa da fitacxen mawakin nan na Amerika Akon da kuma Shahararren Ma shiryin shirya fina-finan dan asalin Najeriya Jeta Amata suka gayyace ta bayan koran da hadakar Kungiyar masu shirya fina-finan Hausa MOPPAN sukayi mata a farkon wananna watan.

  MOPPAN kungiyace dake ladaftar da duk wani wanda yayi ba dai dai ba daga dukkannin kungiyoyin gamayyar fina-finai da wakoki, adan haka ne wannan kungiya ta dauki matakin dakatar da ita a cewar kungiyar an sameta laifuffuka sau hudu.

  Bayan dakatar da ita ne fitaccen mawakin Turanci na Kasar Amuruka Akon wanda dan asali Kasar Senegal ne dashi da fitaccen Maishirya fina-finai Jeta Amata wanda dan Kasar Najeriya inda suka gayyaci Rahama Sadau domin yin aiki tara a shafukansu na twitter.

  Dan gane da wannan gayyata ne Babban Malamin Addinin Musuluncin nan Malam Aminu Daurawa dake Jahar Kano a Najeriya inda ya ja hankalin jarumar da karta amshi gayyatar zuwa da mafi dacewa da ita shine tayi aure domin haka Addinin musulunci ya tanadar a matsayinta na Musulma

  Yanzu dai haka Rahama Sadau na Los Angeles wanda zasu fara aikin fim din Jeta Amata mai suna "The American King."
  (Daga Kannywoodtoday)

  HOTUNAN RAHAMA SADAU A KASAR AMURUKA KENAN.

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: RAHAMA SADAU TA DIRA AMERICA Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama