Wanna
hoton yaran iyamirai ne a lokacin yakin Biyafara
|
A
yayin da hakuri da juna ya faskara a tsarin hakikanin zamantakewa tsakanin
inyamirai karkashin jagorancin dan ta kife,dan tawaye da bijire wa gaskiya
watau Odamegu Ojuku wanda ya ayyana ballewa daga Najeriya,wanda hakan
ya jawo yakin basasa a Najeriya kuma sakamakon hakan ya haifar da matsanancin
yunwa a kasar ta Biyafara.
Wannan
kira ne ga yan hankoren sai sun balle daga Najeriya ta hanyar tarzoma don su kafa kasar su
ta Biyafara cewa basu san me ake nufi da yaki bane,kuma ai ko a wancan
lokacin yan Arewacin kasar nan da ke cikin soja hakuri sukayi da
wulakancin da hafsosin soja yan kabilar inyamurai suka yi ta yi
masu,amma martanin da sojoji yan arewa suka mayar wa inyamuran daga baya,ya nuna masu cewa kasar
Arewa ba kanwar lasa bace.
|
Tags:
TARIHI