• Labaran yau

  October 24, 2016

  Hotuna:Ya kashe matar sa da diyar sa wai don baya iya ciyar da su

  Wani mutum mai suna Dominic Iyayi Ogar dan asalin kauyen Okpoma a karamar hukumar Yala da ke jihar Cross rivers ya kashe matar sa da 'yar sa guda daya tilau da Allah ya ba su.Matar ta sa mai suna Amago 'yar shekara 27 da diyar tasu mai suna Blessing 'yar shekara biyu sun gamu da ajalin su ne ranar 8/10/2016 a kauyen Mpape da ke babban birnin tarayyan Najeriya Abuja.
  Sunday sun ta rubuto cewa,a ranar da Ogar ya aikata wannan danyen aikin,sun kwanta su uku,matar tasa,shi da 'yar tasu a gado daya,wanda da tsakiyar dare ne ya tashi ya daba wa matar sa wuka,da kuma diyar tasu har sai da suka mutu,bayan haka kuma ya dauki gawarwakin ya kai wani paramare ya jefar da su,bayan ya rubuta wata yar takarda ya jefa kusa da gawakin wanda ke nuna cewa bazai iya ci gaba da ciyar da su ba don haka ya aikata wannan danyen aikin.
  Tuni dai wannan mutum ya shiga hannun 'yan sandan babban birnin tarayya Abuja kuma suna gudanar da bincike.


  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Hotuna:Ya kashe matar sa da diyar sa wai don baya iya ciyar da su Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama