Gyaran Najeriya ba aikin mutum daya bane

Baba Bukari
A yayin da tattalin arzikin Najeriya ya shiga halin ni'yasu sabo da hauhawan dalan Amurka da faduwar kudin gangan mai warwas a kasuwannin duniya,ta hakan kuma ya haifar da tsadan rayuwa ga talakan Najeriya.Duk da hakan ya kamata jama'a su sani cewa wanna gwamnati ta shigo cikin wani yanayi da babu gwamnatin Najeriya da ta taba shiga dangane da tattalin arziki  inda gwamnatocin baya sun yi sa'a a wancan lokacin gangan mai ya kai har dala 149 a kasuwar hada hadar man fetur,amm a yanzu gangan mai ana sayarwa ne akan dala 42,ka ga dole a sami matsala a kasafin kudin shiga da yadda za'a tallafa wa rayuwa.

Don Allah a taimaki kasannan ta hanyar ba da gudunmuwa da ingantattun shawarwari ga mahukunta don neman samun nassara da sauki ga talakkan Najeriya wanda idan dai ka samar masa da wutan lantarki,titin mota ,ruwan sha da ingantaccen asibiti da makaranta don yaran shi,to ka gama taimakon shi.To amma har yanzu shi dai talaka na kan kuka a wajen da bai kamata ace yayi kuka ba.Mahukunta,ku duba don Allah.
Gyaran Najeriya ba aikin mutum daya bane Gyaran Najeriya ba aikin mutum daya bane Reviewed by Isyaku Garba on October 10, 2016 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

Powered by Blogger.