Gobara ta kona transfommomin da ke ba Gwadangaji da Tudunwada wuta a garin Birnin kebbi


A ranar Juma'a da misalin karfe 2 na dare ne gabarar wuta ta tashi a cibiyar ba da wutan lantarki a garin Birnin kebbi  kuma ta kona transfomomi guda biyu 7MVA da ke ba Gwadangaji da anguwar Tudunwada wuta wanda hakan ya haifar da rashin wutan lantarkin a wadannan anguwannin.

Tuni dai mai girma Gwamnan Jihar Kebbi Sanata Atiku Bagudu ya ziyarci wurin,bayan yayi  jaje ya kuma nuna damuwar shi kan irin mawuyancin halin da al'umman Gwadangaji da Tudunwada suka shi ga saboda rashin wutan lantarkin a sanadin wannan al'amarin.Ya kuma bukaci hukumar wutan lantarkin ta dauki matakin gaggawa dan ganin an shawo kan wannan lamarin.


Ina fatar za'a shawo kan wannan lamarin cikin karamin lokaci don jama'a su ci gaba da more rayuwar su da wutan lantarki.
Gobara ta kona transfommomin da ke ba Gwadangaji da Tudunwada wuta a garin Birnin kebbi Gobara ta kona transfommomin da ke ba Gwadangaji da Tudunwada wuta a garin Birnin kebbi Reviewed by on October 15, 2016 Rating: 5

ISYAKU TV

Powered by Blogger.