Duba Takardun Mota Ba Aikin ‘Yan Sanda Ba Ne – AIGMataimakin Sufeto Janar na ‘yan sandan Nijeriya, Mr Dan Bature kuma shugaban hukumar na shiyya ta 11 da suka hada jihohin Oyo, Osun da kuma Ondo, ya bayyana cewa, binciken takardun mota musamman a manyan hanyoyi da jami’an ‘yan sanda su ke yi ya sabawa dokar hukumar.
Bature, ya bayyana hakan ne yau Laraba  a jihar Oyo yayin wata ziyarar kwana  biyu da ya kai jihar.
“Aikin ‘yan sanda shine su tabbatar da an samu hanyar da jama’a za su gudanar da harkokinsu ba tare da wata matsala ba” inji Bature.
Bature, ya kara da cewa, bai kamata a ce duk inda motar ‘yan sanda ta ke ta zama wurin cinkosan ababen hawa ba.
Daga Leadership Hausa
Duba Takardun Mota Ba Aikin ‘Yan Sanda Ba Ne – AIG Duba Takardun Mota Ba Aikin ‘Yan Sanda Ba Ne – AIG Reviewed by Isyaku Garba on October 21, 2016 Rating: 5

No comments:

Rubuta ra ayin ka

Powered by Blogger.