• Labaran yau

  October 22, 2016

  Cibiyar Kwankwasiyya ta ba Gwamna Ganduje awa 48 ya cire jar hula ko ya fuskanci shara'a


  Cibiyar Kwankawasiyya da ke Jihar Kano ta ba Gwamnan Kano Dr.Abdullahi Umar Ganduje awa 48 ya cire kuma ya daina amfani da jar hula ko su gurfanar da shi a gaban Kotu.

  Alhaji Shehu Garba Gwammaja ne dai ya shida haka a yayin bikin murnar cika shekara 60 ga uban tafiyar kuma wanda ya kirkiro Kwankwasiyya watau Senator Musa Kwankwaso,Shehu Garba ya ce Ganduje ya ci amanar Kwankwasiyya don haka dole a kyamace shi.Ya kara da cewa tun farko sun yi masa tayi naira miliyan daya domin ya cire jar hular sa amma ya ki,saboda haka basu da zabi face su gurfanar da shi a gaban kotu saboda albarkacin jar hular Kwankawasiyya ne ya sa aka zabe shi daga baya ya ci amanar Kwankwasiyya.
  Ya kuma roki jama'ar jihar Kano da su yafe masu kan kuskuren da suka yi na kawo masu Ganduje,yana mai cewa za su gyara kurakuran su a zabe na gabaci
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Cibiyar Kwankwasiyya ta ba Gwamna Ganduje awa 48 ya cire jar hula ko ya fuskanci shara'a Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama