• Labaran yau

  October 29, 2016

  ANGUWAN GO SLOW BIRNIN KEBBI: PON.A.KANGIWA,LIKITAN JAMA'A

  PON. A.KANGIWA

   DR A.KANGIWA (PON) kwararren likita ne da ke babban assibitin Sir Yahaya da ke garin Birnin kebbi,kuma daya daga cikin kwararrun likitocin fida,ko kuma a ce tiyata da ke wannan assibitin.Abin da ke burge ni game da wannan bawan Allah shi ne yadda ya sadaukar da kan sa wajen taimakon al'umma kuma cikin sauki da ingantaccen kulawa tamkar a assibiti kake,kuma a tsari mai kyau.
  Idan ka je titin anguwar go slow bayan sallar isha'i,ko ba'a gaya maka ba lallai zaka fahimci cewa awai wani mai taimaka wa al'umma a wannan titin a likitance,saboda jama'a da za ka gani suna jiran layi ya zo kan su.Ni dai wannan al'amari ya kayatar da ni domin ya kawo sauki ta hanyar rage wahala da mata da yara suke sha wajen bin layi a wasu assibitoci a kan curutoci kamar mura,zazzabi, da sauran su.

  Wannan lamarin ya zama kalubale gareku likitoci ku yi koyi da wanna talikin,idan da zamu sami wasu likitoci da zasu kwaikwayi abin da PON A.KANGIWA ke yi na taimako a anguwannin su,misali a sami daya a Illela yari,daya a Badariya,daya a Rafin Atiku,daya a Nassarawa 1 da 2,daya a Bayan kara,lallai da hakan zai samar da sauki ga al'umma sannan kum ita gwamnati sai ta sa hannu wajen samar da taimakon gaggawa na kananan magunguna cikin rahusa da na'urorin binciken lafiya na tafi da gidan ka.

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: ANGUWAN GO SLOW BIRNIN KEBBI: PON.A.KANGIWA,LIKITAN JAMA'A Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama