• Labaran yau

  October 29, 2016

  ALI NUHU DA TAWAGAR WASU FITATTUN JURUMAI, DARAKTOCI DA MASU SHIRYA FINAFINAI NA KANNYWOOD ZASU HADU KASAR INGILA DOMIN KARBAR LAMBOBIN YABO.


  Idan Allah ya kaimu nan da kwanaki biyar, wasu daga cikin fitattun masu shirya fina-finai, daraktoci da kuma jarumai maza, mata  zasu sauka a London domin Kabar lambobin yabo daga wata kungiya mai suna African Voice karo na 20.

  Alokacin kasancewarsu a ingilan  Jamilu  Ahmad Yakaisa ( Dakan Daka) shi ne zai fara karbar wata Lambar yabon ranar 04/11/2016 kafin kuma washe gari su sake karbar sauran lambobin yabon tare da wadanda muka ambata a farko daga Kungiyar African Voice.


  Wadanda zasu karbo wadancan lambobin yabo sun hada da Alhaji Jamilu Ahmad Yakasai ( Dakan Daka), Ali Nuhu, Aminu Saira, Umar  M. Sharif, Zaharaddeen Sani, Nafisa Abdullahi da Hadiza Gabon.

  A bara ne akayi karo na 19 inda wannan kungiya ta karrama wasu fitattun yan fim, daga ciki sun hada Ali Nuhu da Adam A. Zango da dai sauransu.
  (Daga Kannywoodtoday)
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: ALI NUHU DA TAWAGAR WASU FITATTUN JURUMAI, DARAKTOCI DA MASU SHIRYA FINAFINAI NA KANNYWOOD ZASU HADU KASAR INGILA DOMIN KARBAR LAMBOBIN YABO. Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama