• Labaran yau

  October 28, 2016

  ADAM A. ZANGO YA TADA TUBAR SA


  A labarin da Adam A Zango ya wallafa a shafinsa na Instagram na cewa ya jingina fitowa a fina-finan Hausa domin ya karama harkansa na waka tagomashi da kuma mai da hakalinsa kacokan kansa, wanda wannan labarin bai ma masoyansa dadi ba domin yadda suke jin dadin ganin fina-finansa. Da ganin wannan batu sai wakilinmu Abu Fu'ad ya tuntubi jarumin ko meyasa ya dau wannan mataki sai yace "Abu Fu'ad kalmar Jinginewa nada fassara dayawa ko a yau ina iya dawowa ko gobe, kuma yana iya zama shekara ko shekaru ba yadda baya iya kasancewa, kawai ina bukatar naga harkan waka ne ta kara karfi a Arewancin Kasar nan domin inka duba an mana nisa a harkan waka, Alhamdulillah in ka duba fim yanzu tayi karfi ba'a Kasan nan ba harda kasashen duniya ansan da Hausa fim, adan haka ne naga ya dace tunda inada basiran kuma a wakar ma Duniyar waka tanayi damu to da haka ne nake ganin inna dawo da hankali a kai zan taimakawa harkan kaman yadda Allah ya bamu sa'a badan mun iyaba a'a sai dan Allah yasa muna da nasibi akan harkan fim to shima haka wakan ina ganin mawaka zamu kara samun karfi duniya ta san mu kamar yadda ta sanmu a harkan fim din duk da a wakan ma an sammu kuma muna da masoya da dama a cikinta."

  Wasu na ganin wannan na da nasaba da cece kuncen da yayi da wani wanda bai fadi sunansa ba a shafinsa na Instagram a ranan lahadin data gabata akan wai yace shiyafi mai digiri wanda har kafan yada labarai ta bbchausa ta wallafa a cewar Adam A Zango "Idan ka mallaki digiri baka da aiki. Ni kuwa ba ni da digiri amma shekara 12 ina da aikin yi. Ko da kana da aiki idan na rera waka daya zan samu kudin da suka fi albashinka." wanda kafafen yada labaran gida suma suka buga, inda shi kuma ya maida martani akan abinda shafin bbchausa da sauran kafafen yada labaran sukata wallafawa, ganin haka shi kuma jarumin ya maida wa bbchausa a shafin nasa na Instagram da cewa "BBC Hausa bakuyi min adalaci ba. Kamata yayi ku rubuta cewa Adam A. Zango ya caccaki wani dan boko wanda yayi masa gorin ilimi. Don da wani nakeyi wanda ya zageni akan banyi nisa a ilimin boko ba. Ni kuma na maida masa martani a instagram page dina".
  (Daga Kannywoodtoday)
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: ADAM A. ZANGO YA TADA TUBAR SA Rating: 5 Reviewed By: Isyaku Garba
  Koma Sama