Header Ads

Mota mai tuka kanta da kanta

Motoci marasa matuƙa sun fara yawo a kan titunan Singapore, inda mutum kan tsayar da su ya shiga kyauta domin yawo. Hakan dai wani ɓangare ne na gwajin motoci, ko da yake akwai mutum a zaune a kujerar direba. Sai dai motocin da kansu suke tuƙi, matuƙin na lura ne kawai da yadda motar ke tafiyar da kanta, don gudun ɓacin rana. Wani kamfani, nuTonomy da ke da ofisoshi a Amurka da ƙasar ta Singapore ne ke yin wannan gwajin.

No comments:

Rubuta ra ayin ka

Powered by Blogger.