Maza da Mata kimanin 400 sun tube zindir a Britaniya

Wasu daga cikin masu bikin
Kimanin mutane 400 suka tube zindir kuma suka tsunduma a cikin Tekun North Sea mai tsananin sanyi domin tara kudin gidauniyar tallafa wa masu fama da matsalar tabin hankali a Britaniya ranar 25 ga watan Satumba.
Wannan al'amari da ake yi a kowane shekara da farkon bazara shi ne na biyar a cikin shekara biyar da fara yin sa.Wayan da suka shiga cikin wannan bikin dai sun hadu ne a bakin ruwan Druridge,a Norhumberland na kasar Britaniya bayan sun biya PAN12 kafin su fara bikin,wanda kudin aka sanya a asusun tallafa wa masu tabin hankali.
Jax Higginson wanda haifaffen Sunderland ne shine ya kirkiro wannan bikin bayan ya halarci irin wannan bikin a Wales.

No comments:

Rubuta ra ayin ka